News

Duk bala’in da ake ciki a ƙasar nan Kwankwaso ne ya jawo mana – Rarara

Fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya zargi tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, da taka rawa wajen haifar da wasu daga cikin matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Rarara ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawa da SL Update, inda ya ce matsalolin tattalin arziki da na gudanarwa da ake fama da su a ƙasar nan sun samo asali ne daga wasu manufofi da matakan da aka ɗauka a baya.

A cewarsa, ɗaya daga cikin manyan matsalolin shi ne yadda aka riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi a hannun gwamnati maimakon a ba su cikakken ikon tafiyar da kuɗaɗensu domin gudanar da ayyukan raya ƙasa a matakin karkara.

“Kuɗaɗen ƙananan hukumomi su ne jijiyoyin wuya na al’umma. Su ne ke kai ayyukan gwamnati kusa da talakawa a matakin ƙasa. Idan aka hana su kuɗaɗensu ko aka riƙe su, to an tauye ayyukan da ya kamata su kai wa jama’a,” in ji shi.

Mawaƙin ya ce tun lokacin da aka fara wannan tsari ne aka shiga matsaloli da dama waɗanda har yanzu ake fama da tasirinsu a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ya yi ikirarin cewa rashin samun cikakken ikon kuɗi da ƙananan hukumomi ke fuskanta ya janyo tsaikon aiwatar da ayyukan raya ƙasa, musamman a fannoni kamar ilimi, lafiya, samar da ruwa da kuma gyaran hanyoyin karkara.

Rarara ya kuma bayyana cewa idan har ana son a samu ci gaba mai ɗorewa da bunƙasa tattalin arziki a matakin ƙasa, dole ne a bai wa ƙananan hukumomi cikakken ikon gudanar da harkokinsu ba tare da katsalandan ba.

Sai dai kalaman na Rarara na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan tsarin tafiyar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da kuma buƙatar tabbatar da cikakken ‘yancinsu a faɗin ƙasar nan.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rabiu Musa Kwankwaso ko wani daga cikin wakilansa bai fitar da wata sanarwa ko martani kan zarge-zargen da Rarara ya yi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button